Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Axios ta yi ikirarin a cikin wani rahoto cewa Ministan Tsaron Saudiyya Khalid bin Salman ya yi gargadi a cikin wani taron sirri a Washington cewa idan Donald Trump bai aiwatar da barazanar da ya yi wa Iran ba, gwamnatin Iran za ta kasance cikin matsayi mai karfi.
Wannan gidan yanar gizon labarai na Amurka ya gabatar da wannan rahoton yana ambaton abin da ya gabatar a matsayin majiyoyi masu ilimi kuma ya rubuta: Ministan Tsaron Saudiyya ya furta wannan matsayi a bayan rufaffun kofofi wand aya sabawa matsayin Riyadh a hukumance na jaddada kai zuciya nesa da guje wa tashin hankali mai tsanani, da fifita diflomasiyya. Axios ta ga wadannan kalamai a matsayin wata alama ta gibin da ke tsakanin matsayin Saudiyya a bayanar jama'a da qudirinta na sirri kan Iran.
Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da ake kara samun tashin hankali a yankin da kuma karuwar kasancewar sojojin Amurka a Tekun Fasha. Bin Salman ya tattauna yiwuwar ɗaukar matakin soja kan Iran tare da manyan jami'an Amurka, ciki har da sakatarorin harkokin waje da tsaro na Amurka, amma ya bar Washington ba tare da cikakken bayani game da dabarun ƙarshe na gwamnatin Trump ba, a cewar majiyoyin da suka saba da lamarin.
Yanzu haka Saudiyya ta shiga cikin damuwa guda biyu masu karo da juna: a gefe guda, mummunan sakamakon babban rikicin soja a yankin, da kuma qudirinta na cewa rashin ɗaukar mataki bayan barazanar makonni na iya ƙarfafawa Tehran gwiwa.
Your Comment